Jirgin ruwa ya kife a Congo

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jirgin ruwa ya kife a Congo

Rahotanni daga arewa-maso-gabashin Congo na cewa wani kwale-kwale dauke da kayan amfanin gona da kuma mutane ya nutse a ruwa, a inda akalla mutane 30 su ka mutu.

Hukumomin kasar sun ce an kuma samu nasarar ceto mutane sama da 100.

Duk da cewa hadarin ya faru ne tun ranar litinin din da ta gabata, sai a ranar Talata ne aka samu labarin al'amarin.

Labarin ya janwo zanga-zanga daga matasan Isangi, garin da ke bakin ruwan da kwale- kwalen ya nufa.

Rahotanni na nuwa na cewa an kona gine-gine da dama sakamakon zanga-zangar.