'Yar Nigeria ta haihu a jirgin bakin haure

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An gano gawar wani mutum a cikin wani jirgin ruwan

Sojin ruwan kasar Italiya sun ce sun ceto bakin haure 1,300 a ranar Kiristimeti.

Cikin mutanen sun hada da wata 'yar Najeriya wadda ta haihu a daya daga cikin jiragen ruwan da sojin suka ceto a ranar Alhamis.

Mafi yawa daga cikin bakin hauren na cikin jiragen ruwa ne da ke karakaina a nesa da gabar tekun Sicily.

Ministan cikin gidan Italiya ya ce an samu gagarumar karuwar masu neman tsallaka tekun Bahar Rum daga arewacin Afrika.

Kimanin bakin haure170,000 ne suka shiga kasar ta Italiya a wannan shekarar.