An fara shari'ar matar laurent Gbagbo

Simone Gbagbo matar Laurent Gbagbo Hakkin mallakar hoto
Image caption Simone Gbagbo matar Laurent Gbagbo

Matar tshon shugaban kasar Ivory Coast wato Simone Gbagbo ta gurfana a gaban kotu, kan zargin da ake yi matana na hannu rikicin bayan zaben da ya farau shekaru 5 da suka gabata.

Ana dai tuhumar Mrs Gbagbo wacce ake yiwa lakabi da mace mai kamar maza tare da wasu magoya bayan maigidanta Laurent Gbagbo su kimanin 82.

Shi kan sa Mr Gbagbo din na zaman jiran gurfana a kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ICC, kan aikata laifukan cin zarafin bil Adama.

Mutane fiye da dubu uku ne aka hallaka bayan zaben shekara ta 2010 mai cike da takaddama.