Kotu ta bayar da umarnin kama limami

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firaiministan Pakistan Nawaz Sharif

Wani alkali a Pakistan ya bayar da izinin kama malamin nan da ake kira Abdul-Aziz, limamin masallacin Red Mosque da ke Islamabad, babban birnin kasar, wanda ya ki Allah-wadai da harin 'yan Taliban da ya hallaka jama'a.

Ana zargin malamin ne da laifin yin barazana ga masu zanga-zanga, wadanda suka yi bore saboda kin yin Allah-wadai da malamin ya yi, kan wani hari da aka kai a wata makaranta da ke Peshawar a wannan wata.

Fiye da mutane 150 ne suka mutu a harin mafi yawansu kananan yara.

Sheik AbdulAziz dai ya yi watsi da zargin yana mai cewa yana da kwarin gwiwa za a ba da belinsa.