Ana bukin tunawa da tsunami a Indonesia

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Ambaliyar tsunami ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 220

Alummomin kasar Indonesia sun fara bukukuwan wuni daya na cika shekaru 10 da faruwar babban bala'in ambaliyar ruwa daga tekun India, wato Tsunami wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 220.

Dandazon mutane sun hadu a kusa da wajen tunawa da bala'in Tsunami a birnin Banda Aceh dake tsibirin Sumatra.

Bala'in na tsunami a shekarar 2004 ya yi sanadiyyar lalata kusan komai a birnin Banda Aceh.

An gudanar da taron addu'o'i a babban masallacin karni na 19, daya daga cikin 'yan tsirarun gine ginen da ba su fadi ba a birnin na Banda Aceh lokacin bala'in.

Sai dai duk da tallafin biliyoyin daloli da kasar ta samu daga kasashen duniya sakamon bala'in, har yanzu, rayuwar wasu mutane a kasar bata koma dai dai ba.

Kazalika, aikin samar da na'urar gargadi kaucewa wasu bala'o'in, wadda zata ci kudi dala miliyan 400 ya ci karo da matsaloli na almubazzaranci.