Ana addu'oi ga wadanda tsunami ya kashe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsunami na cikin manyan bala'oin da aka samu a duniya

Ana addu'oi na musamman a fadin nahiyar Asia, domin tunawa da bala'in tsunami da aka yi shekaru goma da suka wuce.

Bala'in da ya janyo mutuwar mutane fiye da 220,000 wasu kusan miliyan biyu kuma suka rasa matsugunansu.

Guguwar da ta taso daga tekun Indiya ta afkawa al'umomin da ke zaune a bakin tekun a kasashen Indonesia da Thailand da Sri Lanka da kuma Indiyar.

Wadanda suka tsira dai da dama na tuna abin da ya faru, inda aka binne daruruwan gawawwaki a manyan kaburbura.