Angola na gallazawa 'yan ciranin Afirka

Taswirar kasar Angola Hakkin mallakar hoto
Image caption Taswirar kasar Angola

An tsare 'yan gudun hijirar wadanda mafi yawancinsu sun fito ne daga Afirka ta yamma, sama da dubu uku a tsawon kwanaki goma a babban birnin kasar,Luanda.

Suna tsare cikin matsasi,yunwa da kishirwa, sannan rahotanni na cewa ana azabtar da musulmin cikinsu.

Kasar Angola dai ba ta maraba da masu neman mafaka daga Afirka kasancewarsu marasa kwarewa kuma talakawa, sabanin turawan Portugal wadanda kwarewarsu ta sa kasar ta amince da zamansu.

An maida wasu 'yan ciranin gida, yayinda kuma aka kulle wassun su.