Masar: Tuhumar batanci a kan Musulunci

Fatima Naoot Marubuciya a Masar Hakkin mallakar hoto Fatima Naoot FB
Image caption Fatima Naoot Marubuciya a Masar

Ana zargin Fatima Naoot ne da rashin girmama addinin musulunci bayan ta ce yanka raguna da ake yi a babbar sallah shi ne kisan kiyashi mafi girma da bil'dama ke yi.

Kafofin yada labaran kasar sun ce Fatima ta amince cewa ta wallafa kalaman, sai dai ta ce ba ta yi da niyyar batanci ga musulunci ba.

Yin batanci ga addinin musulunci a kasar Masar dai babban laifi ne da ka iya sa mutum ya yi zaman gidan kaso har na tsawon shekaru biyar.

Fatima Naoot ta yi kaurin suna wajen yin tsokaci kan batutuwa masu sarkakakiya a Masar.

A shekarar da ta wuce a wata hira da ta yi da wani gidan talabijin ta baiyana cewa an tilastawa Masar yin afmani da harshen larabci ne bayan da larabawa suka ci Masar din da yaki