An cafke wani jagoran Al Shabaab a Somalia

Wasu 'yan kungiyar al Shabaab
Image caption 'Yan kungiyar al Shabaab

Kwamishinan 'yan sanda na garin El Waq ya shaidawa BBC cewa ko da yake Mr Hersi yana da 'yar karamar bindiga bai nuna wata turjiya ba wajen kama shi.

A shekarar 2012 gwamnatin Amurka ta ayyana bada tukwicin dala miliyan uku ga dukkan wanda ya bada labarin da zai kai ga gano inda Mr Hersi yake wanda shine shugaban bangaren leken asiri na kungiyar al Shabaab.

A farkon wannan shekarar ya raba gari da tsohon shugaban kungiyar Ahmed Abdi Godane wanda aka kashe a wani farmakin sojin Amurka a watan Satumba.

Ko da yake gagarumin farmakin hadin gwiwa da sojojin kungiyar tarayyar Afirka dana Somalia suka kaddamar a watan Maris ya raunana Al Shabaab, amma duk da haka kungiyar na da sauran karfi inda ta cigaba da kai hari babban birnin kasar.

A ranar Kirsimeti 'yan gwagwarmayar sun yi shigar burtu suka saje a matsayin sojojin gwamnati suka shiga sansanin sojin kungiyar tarayyar Afirka wadda aka tsaurara tsaro a cikinta a birnin Mogadishu suka kaddamar da hari.

Wasu sojojin kungiyar tarayyar Afirka sun rasa rayukansu a musayar wutar da aka kwashe fiye da sa'oi biyu ana fafatawa.