An shawo kan kutsen Xbox da PlayStation

Hakkin mallakar hoto sony

Kamfanin Microsoft da Sony sun kusa kammala gyara hanyar intanet ta na'urar wasanninsu na kwamfuta na Xbox da PlayStation da masu kutse suka haddasa musu.

Harin da aka kai wa hanyoyin intanet na sakko da wasannin ranar Kirsimeti, ya sa aka kasa samun wasannin.

A ranar Asabar, Shafin Xbox Live, ya nuna cewa an yi nasarar dawo da hanyoyin intanet na Microsoft.

Haka shi ma kamfanin PlayStation ya ce, yana samun nasarar magance matsalar, kuma yana godiya ga masu amfani da wasan kan hakurin da suka nuna.

Wani gungun masu kutse a shafukan intanet mai suna Lizard Squad, ya ce shi ya haddasa matsalolin.

Gungun shi ne ya taba kai hari kan rumbunan intanet na kamfanin Sony a baya.

Hakkin mallakar hoto sony

Mutane miliyan 48 ne ke amfani da Xbox Live na kamfanin Microsoft.

Shi kuwa PlayStation na kamfanin Sony yana da mutanen da ke amfani da shi sama da linkin na Xbox, inda suka kai kusan miliyan 110.

Wani mai kutse dan shekara 22 da ya kira kansa dan kungiyar na biyu, da ya yi ikirarin dan gungun Lizard Squad ne, ya ce, sun yi kutsen ne, ''domin za mu iya.''

Haka kuma ya nuna cewa sun yi hakan ne domin su nuna cewa akwai rauni a tsarin kamfanonin biyu.

Mutumin, ya ce, shin lokacin Kirsimeti, lokaci ne da yara za su zauna su yi wasan kwamfuta ko da wani sabon abin wasansu, ko kuma lokaci ne da ya kamata su zauna da iyalansu su yi murnar Kirsimeti?