NATO ta mika ragamar tsaron Afganistan

Hakkin mallakar hoto

Bikin mika ragamar tsaron wanda aka gudanar a asirce saboda fargabar hare-haren 'yan kungiyar taliban, zai bar baya da kura, bisa la'akari da irin karfin da kungiyar 'yan Taliban ta ke kara yi.

An bayyana shekarar 2014 a matsayin wadda tafi kowacce muni a tsawon shekaru 11 ta fannin hare-haren ta'addanci wadanda su ka haddasa mutuwar mutane masu yawa.

Sai dai kuma za a bar dakarun kungiyar ta NATO har 12,000, da kuma karin wasu sojojin na rundunar sojin Amurka domin horas da sojin Afghanistan ta fuskar yakin da ta'addanci.