Libya na zama matattarar 'yan ta'adda - Faransa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kasar Faransa ta yi gargadin cewa Libya na zama matattarar 'yan ta'adda.

A cewar Ministan tsaron kasar Yves Le Drian, mayakan IS masu da'awar kafa daular musulunci, suna hada kai da tsoffin abokanan hamayyarsu na Al Qaeda.

Minsitan ya kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Afrika, da su tashi tsaye wajen ganin an tunkari wannan matsala a shekara mai zuwa.

Ya kuma kara da cewa, taruwar gungun 'yan ta'adda kusa da yankin Meditareniya, babbar barazana ce ga kasar Faransa.