An toshe hanyoyin samun Gmail a China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu amfani da intanet a Chinan sun kasa samun hanyoyin shiga Gmail da sauran shafukan Google

Rahotanni daga masu amfani da intanet a China na nuna cewa ba sa iya samun shiga akwatinsu na wasikun email na kanfanin Google, wato Gmail.

Shiga shafin wasikar na Google wato Gmail abu ne da ya gagara a kwanakin nan a kasar, to amma jama'a kan yi amfani da wasu hanyoyin irin su Microsoft Outlook su shiga.

Sai dai kuma a yanzu masu wannan kewaye sun ce hakan ma ya gagara, inda alamu ke nuna cewa an datse hanyoyin.

Haka shi ma kamfanin na Google ya gano cewa ya samu raguwar masu amfani da shafin matuka, kuma har yanzu lamarin bai sauya ba.

Kamfanin na Amurka ya ce babu wata matsala ta na'ura da ya san yana fama da ita kan samar da Gmail a Chinan.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A 2010 dangantaka ta tabarbare tsakanin Google da hukumomin China

Mai magana da yawun Google a yankin Asia da Pacific Taj Meadows, ya sheda wa kamafanin dillancin labarai na Associated Press, ''ba mu da wata matsalar na'ura.''

Kungiyar kare hakkin masu amfani da intanet, GreatFire.org ita ce farkon kungiyoyin da suka bayyana matsalar.

Gwamnatin China ba ta tabbatar ko musanta cewa ita ke da hannu wajen datse hanyoyin samun Gmail din ba.

Kamfanin Google ya rufe ofishinsa na China a 2010, sakamakon rashin jituwa da hukumomin kasar, kan matakan sanya ido ko takaita harkokin intanet da gwamnati ke yi