Kano: An samu rarrabuwar kawuna a jam'iyar APC

Nigeria
Image caption Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da jam'iyar APC ke mulki a Najeriya

An samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Kano dangane da batun zaben wanda zai zamo mataimakin gwamna.

A baya dai wasu rahotanni sun ce an yi alkawarin bayar da wannan mukami ga Abdurrahman Kawu Sumaila daya daga cikin wadanda suka yi takarar neman kujeran gwamnan.

Sai dai daga bisani wasu rahotanni sun ce ya janye, bayan yarjeneiyar da aka cimma da shi.

To amma a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC Kawu Sumailan, ya ce ba janyewa ya yi ba, an hana shi mukamin ne kawai.

Ya kuma kara da cewa bai yi mamaki ba na rashin bashi matsayin mataimakin.