Kamfanin Uber ya yi nadamar kara kudin sufuri

Uber Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kamfanin Uber ya ce zai maido mutanen da lamarin ya shafa kudadensu

Kamfanin Uber mai sufuri ya ba da hakuri kan karin kudin farashin sufuri da ya yi a lokacin harin Sydney.

Yayin da aka kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku a Sydney da ke Australia, kamfanin ya kara kudin ninki hudu a lokacin da mutane ke kokarin su tsere daga yankin da lamarin ya auku..

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da kasar Korea ta Kudu ke tuhumar kamfanin da karya dokar kasar ta hanyar yin amfani da motocin kansa.

A Korea ta Kudu doka ce motocin sufuri su kasance na kasa ne ba mallakar masu sufurin ba.

Wannan takaddama itace ta baya - baya nan da ta rutsa da kamfanin na Uber.

Tsari ne a kamfanin sufurin idan fasinja ya kira motar sai direba ya yi lissafin kudin da za a caji fasinjan.

A ranar da aka kai harin na Sydney, kamfanin ya sha suka matuka a shafukan sada zumunta.

Hakan kuma ya sa motocin kamfanin suka yi ta daukar fasinja kyauta domin a rarrashi al'uma.