Shekara guda da tsare 'yan jaridar al-Jazeera

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin hukumomin Masar da kokarin rufe bakin 'yan jarida

Iyayen daya daga cikin ma'aikatan al-Jazeera uku da aka kama a Masar sun ce sun yi ammanar za a sako su nan bada jimawa ba.

A hirarsa da BBC shekara guda bayan kama 'yan jaridar, mahaifin Peter Greste ya ce babu tantama za soke hukuncin kotun da aka yanke musu.

An yanke wa Mr Greste da Mohammed Fahmy da kuma Baher Mohammed hukuncin daurin shekaru bakwai zuwa 10 a watan Yunin bana bisa zargin yada labaran karya da taimakawa kungiyar 'yan ta'adda.

A cikin wannan makon, wata kotu a Masar za ta yanke hukuncin ko suna da damar daukaka kara.

'Alaka da Muslim Brotherhood'

'Yan jaridar sun karyata zargin da ake musu na hudda da haramtaciyyar kungiyar Muslim Brotherhood bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohammed Morsi a bara.

A cewarsu sun yi aikinsu ne kawai ba tare da son zuciya ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan jarida a duniya na mara baya ga ma'aikatan al-jazeera

Abokan Mr Greste, wanda dan kasar Australia ne kuma tsohon ma'aikacin BBC, da Mr Fahmy wanda dan Canada da kuma Mr Mohammed dan kasar Masar sun yi bikin tunawa da tsare abokan aikinsu a ranar Litinin.

Hotuna a dakunan watsa labarai na al-Jazeera sun bukaci Masar ta sako ma'aikatan inda a turance aka rubuta "Free them now".

Sannan 'yan jarida a duniya sun ci gaba da amfani da "#FreeAJStaff" da "#JournalismIsNotACrime" a shafukan Twitter domin matsin lamba ga hukumomi a Masar su sako 'yan jaridar.