An bukaci a saki dan jaridar Al-Jazeera

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumomin Masar sun zarge su da goyon bayan ta'addanci da watsa labaran karairayi

Maihaifan dan jaridar Al-Jazeera, Peter Greste, da aka aka a Masar sun roki hukumomin kasar su sake shi shekara daya bayan an kama shi.

A ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2013 ne aka kama Mr Greste da abokan aikinsa Mohamed Fahmy and Baher Mohamed bisa zargin watsa labaran karya da goyon bayan 'yan ta'adda.

Sai dai ma'aikatan sun musanta hakan, suna masu cewa suna bayar da rahoto ne kawai kan yadda kungiyar 'yan Uwa musulmai take gudanar da ayyukanta a kasar.

Gidan talabijin na Al Jazeera ya ce ma'aikatansa a ko'ina cikin duniya za su yi jimanin ci gaba da tsarewar da ake yi wa abokan aikinsu shekara daya cur ke nan.