Rikici a kusa da fadar shugaban Gambia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jammeh ya dade a kan mulki

Rahotanni daga Banjul babban birnin kasar Gambia na cewa an shafe daren jiya ana musayar wuta a kusa da fadar shugaban kasar.

Rikicin ya barke ne a daidai lokacin da shugaban kasar Yahya Jammeh yake ziyara a kasar Faransa.

Rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce an dakile yinkurin juyin mulkin soja ne da wasu sojoji suka yi bore.

Shugaba Jammeh ya shafe shekaru 20 a mulkin kasar tun bayan da ya yi juyin mulki.

Ana zargin shugaban da take hakkin bil adama da kuma gallazawa jam'iyyun adawa da kafafen yada labarai a kasar.