Kotu ta koka kan kudaden shigar Niger

Niger Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An shawarci ma'aikatu mallakar gwamnati da su dinga bin ka'idojin amfani da kudade

A Jamhuriyar Nijar, kotun kula da sha'anin kudi ta kasar ta ce akwai kura-kurai game da yadda wasu hukumomi na gwamnati ke gudanar da ayyukansu.

A cewar kotun ana tafka kura-kuran ne a fannin kudaden shiga na aljihun gwamnati.

Galibin hukumomi da kamfanonin da kotun ta yi nazari a kansu dangane da yadda suka sarrafa kudaden kasafin kudi na shekarar 2012, ba sa bin doka da oda a cewar kotun.

Kotun kula da sha'anin kudin ta Nijar ta bayyana wannan matsayin nata ne a cikin rahotonta na 2013 da ta wallafa jiya a Yamai.

Yanzu haka kotun ta yi kira ga hukumomin da su yi gyara kan yadda suke tafiyar da ayyukan na su.