Fina-finan da aka fi satar fasaharsu a 2014

Piracy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An sauke bidiyon fim din Wolf of Wall Street sau miliyan 30 a wannan shekarar

Wani bincike ya gano cewa fim din "Wolf of Wall Street," shine wanda aka fi satar fasaharsa a shekarar 2014 mai karewa.

Kamfanin Expicio mai bin diddidin fina-finan da aka saci fasaharsu ya ce fim din zane na "frozen" shine na biyu.

Mujallar Hollywood Reporter wacce ta dauko rahoton sakamakon binciken ta ce an sauke fina-finan biyu sau miliyan 30 a intanet a tsakanin watan daya ga Janairu zuwa ranar 23 ga watan Dismba.

Fim na uku da aka fi satar fasaharsa a cewar mujallar, shine na "gravity."

Ya kuma bi bayan fim din Frozen ne inda ya aka sauke shi sau miliyan 29.357.

Wolf of Wall Street, wanda ke dauke da gwarzon dan wasan nan Leonardo DiCaprio ya sha suka a lokacin da aka fitar da shi, saboda yawan amfani da muggan kwayoyi da hotunan batsa da aka nuna.

Fim din kuma ya samu damar shiga jerin wadanda aka zaba domin karbar kyautar Oscars a matsayin fim din da ya fi kyawun hotuna.

Sauran fina-finan da aka saci fasaharsu da dama a shekarar ta 2014 sun hada da "12 Years a Slave" da " American Hustle" da kuma "Captain Philips."