'Yan gudun hijira za su tagayyara a 2015

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mr Guterres ya ce ba za su iya biyan bukatun 'yan gudun hijira ba

Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce 'yan gudun hijirar za su sha bakar wuya a 2015.

Antonio Guterres ya yi gargadin cewa hukumarsa za ta fuakanci karancin kayayyakin da za ta bai wa 'yan gudun hijirar a 2015 yayin da take kokarin tunkarar abin da ya kira gagarumin karuwar bukatar kayan tallafi a fadin duniya.

Mr Guterres ya shaida wa BBC cewa da wuya rikice-rikicen da duniya ke ciki su ragu, kuma hukumarsa ba za ta iya samar da ko da rabin kayayyakin da za ta tallafa wa 'yan gudun hijirar ba.

Ya bayyana cewa akwai karuwar mummunan rikici a kasashen Syria da Iraq da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Africa ta Tsakiya da Nigeria da kuma Ukraine.