An rantsar da sabon shugaban Tunisia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Essebsi ya zama shugaban farko da aka zaba a mulkin dimokaradiyya

An rantsar da Beji Caid Essebsi a matsayin sabon shugaban Tunisia da aka zaba a karkashin mulkin dimokaradiyya na farko a kasar.

An rantsar da shi ne a ginin Majalisar Dokokin kasar da ke birnin Tunis.

Mr Essebsi -- mai shekaru 88 a duniya -- ya lashe zaben kasar wanda aka je zagaye na biyu a watan jiya.

Rantsuwar da ya sha ta bude sabon babin siyasa a kasar, shekaru hudu bayan an tunbuke shugaba Zine el-Abedine Ben Ali, lamarin da shi ne ya yi sanadiyar boren da aka yi a kasashen Larabawa.