Tsuntsaye sun ga alamar mahaukaciyar guguwa

Tsuntsaye Warbler Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Tsuntsaye Warbler

Masana kimiyya a Amurka sun ce adanannun bayanai da aka bincika sun nuna cewa wani jinsi na tsuntsaye da ake kira warblers sun tsere daga gidajensu kwana daya gabanin isowar mahaukaciyar guguwar da ta yi barna a Amurka cikin watan Aprilu na shekara ta 2014.

Tsuntsayen dake nuna yanayi sun nuna cewar wannan jinsin na tsuntsayen sun arce daga gidajensu suka yi tafiyar kilomita dari bakwai zuwa kudancin tekun Mexico.

Kwana daya bayan arcewar ta su, mahaukaciyar guguwa da ruwan sama suka yi kaca-kaca da kudanci da tsakiyar Amurka.

A bayanan da suka rubuta a mujallar kimiyyar sanin yanayin halitta, masana yanayi sun nuna cewar wadannan tsuntsayen da wasu takwarorinsu mai yiwuwa sun tsinkayi bala'in dake tafe da 'yan kunnuwansu.

Jinsin tsuntsayen Warblers sun kammala kaurar da su kan yi saboda yanayi 'yan kwanaki kafin afkuwar lamarin, sun dawo har sun fara yin sheka bayan tafiyar kilomita dubu biyar daga Colombia.

Dr Henry Streby na jami'ar California Berkeley ya ce da farko ya kwatanta ne ya ga ko bin diddigin jinsin tsuntsayen Warblers zai ma yiwu.

Dr Streby ya gaya ma BBC cewar wannan yanayi na gwaji ne ga wani babban bincike da muke so mu gudanar.

"wadannan dai, wasu kananan tsutsaye ne masu kuka tamkar suna waka, girmansu bai wuce gram 9 ba.

Kasancewar sun koma yankin da wadannan tsuntsaye masu tabbatar da hasashen yanayi, shine abinda za a ce babbar nasara ce ta wannan yanayi. Sai kuma ga abinda ya faru.

Karin bayani