An kashe mutane 15 a kusa da Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kashe 'yan banga da masu gadi

Maharan da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun kashe akalla mutane 15 lokacin da suka kai hari a kauyen Kautikari da ke jihar Borno ta Najeriya.

Rahotanni sun ce maharan sun je garin ne a kan babura, kuma sun kashe masu gadi da 'yan banga da dama.

An kai harin ne ranar Talata da asuba.

Kauyen na Kautikari yana kusa da garin Chibok inda 'yan Boko Haram suka sace mata fiye da 200 a watan Aprilu.

A wannan shekarar kawai, Boko Haram ta kashe fiye da mutane 10, 000 a Najeriya, kuma har yanzu gwamnati ta kasa shawo kan lamarin.