Ghana ta rusa Kungiyar masu tsaurin ra'ayi

'Yan kungiyar Musulmi da aka rusa a Ghana Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan kungiyar Musulmi da aka rusa a Ghana

A kasar Ghana wasu shugabannin addinin Islamar kasar sun fara nuna damuwa bisa kafa wata kungiyar sintiri a Zangon garin Akim- Ofuwase dake jihar Gabashin kasar, da ake kwatantawa da kungiyar Boko Haram.

Jiya ne dai Hukumomin 'yan sandan kasar suka umarci shugabannin al'ummar Musulmin garin da su rusa kungiyar, saboda aikace- aikacenta da ake zargin sun hada da yiwa mutane bulala, sun saba-wa dokokin kasar.

A yanzu haka dai al'ummar Musulmin kasar sun tashi tsaye don ganin cewa ba a samu bullar masu cusawa matasa irin wadannan ra'ayoyin da za su kai ga kafa irin wadannan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayin addinin Musulunci a cikin kasar ba.

Sheik Sha'aibu Abubakar ,daya cikin shugabannin addinin Islaman kasar, ya yi ma BBC karin bayani kan matakan da suke dauka.

Karin bayani