Batun 'yancin Palasdinawa ya sha kasa

Ban ki Moon da Mahmud Abbas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ban ki Moon da Mahmud Abbas

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da wani daftarin kudurin Palasdinawa da kasar Jordan ta gabatarwa kwamitin, wanda yayi kira da a kawo karshen mamayar da Isra'ila take yi a yankin palsdinawa cikin shekaru 3.

Wannan Kudurin dai bai samu kuri'u Taran da ake bukata ba, saboda Kasashe takwas ne suka aminta da kudurin, sannan biyar suka kauracewa zaben

To, sai dai kasar ta Jordan ta ce kuri'ar da ka kada, ba zata dakatar da yunkurin da ake na warware rikicin ba.

Karin bayani