Mutane dubu 70 suka mutu bara a Syria

Barnar yaki a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barnar yaki a Syria

Masu fafutikar kare hakkin Bil Adama na ikirarin cewar bara, yakin basasar Syria yayi sanadiyar asarar rayukan mutane fiye da dubu 70 -- kusan dubu 18 fararen hula ne.

Galibin mutanen da suka mutu a bara din dai dakarun gwamnati ne da mayakan yan tawaye da kuma yan gwagwarmaya masu ikirarin jihadi.

Kasar Amurka da kasashen Larabawa sun ci gaba da kai hare hare da jiragen yaki a kan kungiyar kasar musulunci ta IS.

Mutane fiye da dubu dari biyu ne aka kashe tun soma rikicin kasar Syrian shekaru hudu da suka wuce.

Haka nan kuma ya haddasawa mutane kusan miliyan ukku gudun jihira.