An yi wa mutane yankan rago a Kamaru

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Gwamnatin Kamaru ta sa kafar wando daya da 'yan Boko Haram

'Yan kungiyar Boko Haram sun hallaka fasinjoji a garin Waza na lardin arewa mai nisa a jamhuriyar Kamaru.

Ana zargin 'yan Boko Haram sun yi wa motar fasinjoji da ta taso daga Kousseri inda ta nufi birnin Maroua kwanton bauna inda suka yi wa mutane yankan rago.

Lamarin ya sa al'ummar yankin sun shiga wani hali na gigita da kuma zullumi.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai kan adadin wadanda suka rasu ko kuma suka samu raunuka.

A cikin 'yan watannin nan 'yan Boko Haram sun hallaka mutane da dama a Kamaru.