Sabon binciken masana game da Kansa

Cutar Kansa ta fatar jiki Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Cutar Kansa ta fatar jiki

Wani sabon bincike ya nuna cewa mafi yawancin nau'oin cutar sankara ko Kansa na samuwa ne sakamakon rashin sa'a, a madadin ace daga kwayoyin halitta ne, ko muhalli ko kuma irin yadda dan adam yake rayuwa.

Masu bincike a Amurka sun yi nazari a kan na'uoin cutar kansa guda 31, sannan suka gano cewa kashi biyu bisa ukunsu, rarrabuwar kwayoyin halitta ne ke hadadda su.

A kowacce rabuwar kwayar halitta akwai hatsarin samun canji wanda zai kai ga kamuwa da cutar kansa.

Masana kimiyyar sun bayar da shawarar cewa kyautata yanayin rayuwa da muhalli na taimakawa wajen kare cututtuka kamar cutar dajin da ta shafi huhu ko ta fatar jiki.

Karin bayani