Kotu ta dakatar da dokar tsaro a Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Kenyatta na fuskantar matsi a kan dokar

Babbar kotu a kasar Kenya ta jingine wani bangare na wata sabuwar dokar tsaro mai cike da rudani har sai zuwa lokacin da karar da 'yan adawa suka shigar wacce ke kalubalantar dokar ta fito.

An gabatar da dokar ce makonni biyu da suka gabata a lokacin zaman majalisa wanda ya juye zuwa fada.

Ministocin kasar sun ce dokar za ta taimaka wajan yaki da kungiyar Al-Shabbab.

Amma 'yan adawa sun musunta cewa ayoyin dokar kamar su daure wanda ake zargi har tsawon shekara daya ba tare da tuhuma ba ya keta hakkin dan adam.