Rundunar sojin Nigeria ta kori sojoji 203

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga Nigeria sun ce rundunar sojin kasar ta kori wasu sojoji 203 bayan wata kotun soji da ta yi zama a asirce ta same su da laifi.

Ana zargin sojojin ne dai da kin bin umarnin da kwamandansu ya ba su na shiga fagen fama a garuruwan Bama da Gwoza, wadanda ke karkashin ikon mayakan kungiyar Boko Haram.

A watan Disamba ma, wata kotun soji da ta yi zamanta a Abuja ta yanke wa wasu sojoji sama da 50 hukuncin kisa, bayan ta same su da laifin bijirewa umarni.

Har yanzu dai hukumomi ba su tabbatar da wannan labari a hukumance ba, saboda kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriyar, Birgediya Janar Olajide Laleye, ya shaida wa BBC cewa ba zai iya tabbatarwa ko musanta labarin ba a wannan lokaci.

Sai dai kuma wata majiyar tsaro ta tabbatar wa BBC cewa an kori sojojin ko da yake majiyar ba ta tabbatar da adadin wadanda aka kora ba.

Daya daga cikin kafofin yada labarai na kasar ta intanet, Premium Times wacce ta buga labarin, ta ambato daya daga cikin sojojin yana cewa an tsare su har tsawon kwanaki 90 a birnin Bini na Jihar Edo kafin a yi musu shari'a da tsakar dare, a kuma kore su.