An kashe mutane tara a rikicin Filato

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jihar Filato na fama da rikicin kabilanci

Rahotanni daga Jihar Filato na Nigeria sun ce mutane kusan 9 ne aka kashe a wani sabon rikicin kabilanci a karamar hukumar Mangu.

Tashin hankalin ya faru ne tsakanin Fulani da 'yan kabilar Maghavul.

Lamarin ya janyo an kona bukkoki da yawa.

An dade ana fama da rikicin kabilanci a jihar Filato lamarin da ya janyi mutuwar dubban mutane.

A wani labarin kuma jami'an tsaro a Jos babban birnin Jihar ta Filato sun kwance wasu bama bamai da aka ajiye a kusa da gidan wani babban malamin kungiyar Izala.

Bama baman ba su tashi ba.