Sarki Abdullah na fama da ciwon huhu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarkin Abdullah

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ta ce Sarki Abdullah na fama da cutar da ke da nasaba da huhunsa.

Bayanai sun ce an saka wa Sarkin wani bututu a cikin jikinsa domin taimaka masa nunfashi.

Kamfanin dillancin ya ambato kotun masarautar na cewa an samu nasarar tiyatar sannan kuma Sarkin na samun sauki.

Kwanaki biyu da suka wuce ne aka kwantar da Sarki Abdullah mai shekaru 90 a asibiti.

Tun a shekera ta 2005 ne Sarkin ya dare kan karagar mulki.