An kai mummunan hari a Baga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane da yawa sun halaka a sabon hari a Baga

A Najeriya, rahotanni daga jihar Borno a arewacin kasar na cewa mutane da yawa da suka hada da mata da yara kanana sun halaka yayin da suke kokarin tserewa ta kogi daga hare-haren kungiyar Boko Haram a garin Baga ranar Asabar.

Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram sun yi zugar da basu taba yin irinta ba a garin, inda suka yi ta kashe mutane, tare da yin bata kashi da sojoji.

Rahotannin sun ce daruruwan mutane ne suka kwana a cikin tabkin Chadi, yayin da wasu suka nutse a ruwa.

Cikin wuraren da 'yan kungiyar suka kaddamar da hare-haren, har da sansanin jami'an tsaro na hadin gwiwa tsakanin kasashen Najeriya da Chadi da Nijar dake Milfo, a garin na Baga.

Wasu mazauna garin da suka samu tsallakawa zuwa Chadi sun ce a jejjere kenan 'yan kungiyar na kaddamar da hare hare a garin a 'yan kwanakin nan.