'Yan Boko Haram sun sace matasa 40

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zargin 'yan Boko Haram na amfani da matasan da suke kamawa wajen kai hare-hare

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun yi awon gaba da matasa da yara 40 ranar jajiberin sabuwar shekara a kauyen Malari, na jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Wasu mazauna kauyen da suka tsira sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Asabar cewa mayakan sun yi wa kauyen dirar mikiya cikin motocin a kori-kura da makamai.

Bayan sun yi wa mutanen wa'azi a kofar gidan mai garin, sai suka ware yara maza 'yan shekaru 10 zuwa 23 suka tafi da su.

Ana ganin sun tafi da su zuwa dajin Sambisa ne da ke kusa da kauyen wanda kuma ake ganin shi ne babbar matattarar 'yan kungiyar.

Sai dai kuma labarin sace yaran ya bayyana ne 'yan kwanaki bayan al'amarin sakamakon tsira da wasu mutanen kyauyen da makwabtansu suka yi zuwa Maiduguri ranar Juma'a.

Kauyen na Malari ya na da tazarar kilomita 20 ne daga dajin na Sambisa wanda ya ke kusa da Gwoza, garin da 'yan kungiyar su ka bayyana daya daga cikin daularsu ta Musulunci a watan Yuni.