Italy: Yan fasakwauri na cin kazamar riba

Hakkin mallakar hoto epa

Masu tsaron ruwan Italiya sun ce jirgin ya isa gabar Tekun kasar ne cikin dare, kuma an kwashe dukkan muatanen da ke cikin sa a Bus zuwa wasu sassan kasar.

Sun kuma ce mutanen ba a tagayyare suke ba, duk wahala da suka shiga ta kwanki ukku a tsakiyar Teku, ba tareda wani mataimaki ba.

An dai samu rohotanni masu cin karo da juna akan inda jirgin ya fito. Wani kaulin yace ya taso ne daga Cyrus, yayinda da kuma wasu ke cewa daga Turkiyya jirgin ya taso.

Hukumomin Itlaiyar sun ce wasu masu fasa kaurin jama'a ne suka damfari fassinjojin, suka sauya. Wato maimakon bi dasu ta Libya, inda aka saba, sai bi da su wata hanya.

Hukumomin sun kuma ce wata sabuwar dabarar da masu fasa kaurin suk abullo da ita, ita loda jama'a a a matattaun jiragen ruwa na jigilar kaya, sannan suyi watsi dasu a tsakiyar Teku.

Daya daga cikin fasinjojin ne yayi amfani na'urar sadarwar da ke cikin jirgin ya ankaradda jami'ain tsaron Italiya halin da suke ciki a tsakiyar Teku.