Ebola: Liberia za ta bude makarantu

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Ebola ta hallaka dubban mutane a Liberia

Gwamnatin kasar Liberia ta ce za a bude makarantun kasar a watan Fabrairu mai zuwa.

Wata shida kenan bayan rufe makarantun sakamakon barkewar annobar Ebola.

Wani jami'in gwamnatin kasar ya ce ana shirin rarraba wa makarantun na'urorin auna zafin jiki da kuma bokatai don wanke hannu.

Sama da mutum dubu uku ne cutar Ebola ta halaka a kasar Liberia.

Adadin mutanen da ke harbuwa da cutar na raguwa a cikin 'yan makwannin nan, duk da cewa ana samun bullar cutar a wasu sababbin wurare a yankunan karkara.