An gano kabarin sarauniyar mulkin Fir'auna

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi amanna sarauniya Khentakawess kodai mahaifiya ce ko kuma mata ga Sarki Neferefre

A kasar Masar, masu binciken kan mutanen da suka rayu, sun gano kushewar wata sarauniya da ba a santa ba, wadda ta yi rayuwa a Daula ta Biyar ta zamanin mulkin Fir'auna.

Masu binciken 'yan kasar Czechoslovakia sun gano kushewar ce a wata tsohuwar makabarta a Abu Sir, kudu maso yammacin birnin Cairo.

A cikin kushewar, akwai 'yan zane-zane da suke nuna sunan sarauniyar, Khentakawess.

Masu binciken sun yi amanna, sarauniyar kodai mahaifiya ce ko kuma mata ga Sarki Neferefre na lokacin mulkin Fir'auna, wanda ya ci zamaninsa shekaru 4500 da suka gabata.

Masu bincike sun gano wasu cokula da kwanukan girki kimanin 30 da aka yi su da farin dutse da kuma jar waya data ake narkawa.