Nigeria: Ma'aikatan kotu na yajin aiki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ma'aikatan kotun sun ce bangaren zartarwa ya ki bin umarnin kotu

Kungiyar ma'aikatan kotu a Najeriya sun fara yajin aiki bayan bangaren zartarwa ya ki yin biyayya ga umarnin da wata kotu ta ba shi na daina yin amfani da kudinsu.

Shugaban kungiyar, Mustapha Adamu, ya ce ma'aikatan sun yanke shawarar tafiya yajin aikin sai baba-ta-ganin ne saboda bangaren zartarwar ya karya dokar kotun.

Mustapha Adamu ya jajantawa wadanda suka shigar da kara kan rashin bude kotunan, yana mai cewa ma'aikatan ba su da zabi illa su tafi yajin aikin domin tilasta wa bangaren zartarwa aiwatar da umarnin kotun.

Lamarin dai zai shafi shari'un da ke gaban alkalan kotunan, musamman ganin cewa kasar na fama da cinkoso a gidajen yari.