MDD ta sa baki kan hukuncin kisa a Nigeria

Wata kotun soji a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ta dauki matakan da suka dace don ganin ba a zartar da hukuncin kisan da aka yanke wa sojojin Najeriyan nan guda 54 ba.

An dai yanke wa sojojin hukuncin ne saboda kin bin umarni wajen yakar kungiyar Boko Haram.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan tattara rahotannin da suka jibanci kisan gilla, Christof Heyns, wanda ya bayyana hakan ya ce, majalisar ta na duba yiwuwar tattaunawa da shugaba Goodluck Jonathan kan al'amarin.

Matakin majalisar dai ya biyo bayan wani koke ne da kungiyar kare hakkin dan-adam ta SERAP ta aika wa majalisa