Boko Haram na ci gaba da mamaye Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau ya ce ya kafa 'daular Musulunci'

Rahotanni a Nigeria sun nuna cewa daukacin kananan hukumomin da ke arewacin Borno sun koma karkashin ikon kungiyar Boko Haram.

Hakan dai ya biyo bayan kwace garin Baga wanda da ma shi ne na karshe da ke hannun gwamnati tun bayan da 'yan Boko Haram suka tsananta kai hare-hare a kan yankunan arewa maso gabashin Nigeria.

Image caption Gwamna Kashim Shettima na Borno na cikin matsin lamba

Sanata mai wakiltar Borno ta arewa, Maina Ma'aji Lawal ya ce hare-haren sun janyo al'ummar yankin na zaune cikin mawuyacin hali.

"Abin bakin ciki ne gare ni, babu abinda zan ce sai dai in bai wa mutane hakuri."

Kananan hukumomin da ke arewacin Borno su ne Marte, da Magumeri, da Mobbar, da Gubio, da Guzamala, da Abadam, da Kukawa, da Kag, da Nganzai da kuma Monguno.

'Tsallakawa Chadi'

Mazauna garin Baga wadanda suka tsere cikin kwale kwale zuwa kasar Chadi mai makwabtaka sun ce an kashe mutane da dama, an kuma kona garin, da dama kuma sun rasa rayukansu sakamakon nutsewar da kwale-kwalen ya yi saboda yawan jama'a.

Wani mazaunin garin Baga ya shaidawa BBC cewa "Duka kan iyakokin Nigeria da suka hada da Niger , da kuma Kamaru duk suna hannun 'yan Boko Haram."

Ya kara da cewa " Sojoji da yawa sun yar da makamansu sun gudu tare da sauran jama'a."

Kawo yanzu dai rundunar sojin Nigeria bata ce komai ba a kan harin.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service