Palasdinawa za su ci gaba da fafutika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mahmoud Abbas ya ce ba zai daina gwagwarmaya kan Palasdinawa ba.

Shugaban Palasdinawa, Mahmoud Abbas, ya ce yana duba yiwuwar canza salo wajen sake gabatarwa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya batun kawo karshen mamayar da Isra'ila take yi musu da kuma batun bai wa kasar 'yanci.

A makon da ya gabata ne dai aka dakatar da kudurin, amma an samu sauyi daga hukumar tsaron a farkon shekarar nan.

Shugaba Abbas ya ce za a yi ta gabatar da kudurin har sai an amince da shi.

Amurka dai na kokarin amfani da karfin ikonta domin ta dakatar da shi.