An nada sabon Firayi Minista a Tunisia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption zabe na farko kenan da aka yi bayan juyin juya hali na Tunisia

An zabi tsohon ministan harkokin cikin gida na Tunusia a matsayin sabon Firayi Minista da zai jagoranci sabuwar gwamnatin kasar.

An nada Habib Essid, dan shekara 65, a matsayin sabon Firayim ministan kasar ne bayan yarjejeniya tsakanin jam'iyyun siyasar kasar a sabuwar zababbiyar majalisa.

Shugaban majalisar dokoki Mohamed Naceur, ya ce "Mun zabi Essid ne saboda mutum ne mai tsayuwa da kafufuwansa kuma kwararre ne a bangarorin tsaro da tattalin arziki."

Habib Essid dai ya taba rike wannan mukami na Firayim ministan a kasar ta Tunisia tun zamanin mulkin Zinel Abidin Ben Ali.

Sabon ministan dai na da jan aiki a gabansa na hada kan jam'iyyun siyasar kasar da dama don samun rinjaye a majalisar dokokin kasar.