Masana a Amurka sun gano duniyoyi 8

Hakkin mallakar hoto NASA
Image caption Duniyoyin da aka gano suna da halittu masu kamanceceniya ta duniyar Earth

Masana ilimin taurari a Amurka sun gano wasu duniyoyi guda takwas da suke da halittu masu kama da na duniyarmu.

Masanan sun hango duniyaoyin ne ta yin amfani da na'urar hango halittun sararin samaniya, bayan shekaru 20 suna bincike a kansu.

Masu binciken sun ce akwai yiwuwar a samu duwatsu da tekuna a cikin duniyoyin, kamar yadda duniyar da muke take da su, sannan kuma suma suna da wasu hallittun da za su iya sawa a rayu a can.

Amma kuma duniyoyin takwas kananu ne, domin duniyarmu ta rubanya su sau biyu a girma, sannan kuma basu da matsanancin zafi ko sanyi.

Sai dai masanan ba su fadi ko akwai wata daga cikin duniyoyin da bil'adama zai iya rayuwa a cikinta ba, sai dai sun nuna hakan abu ne mai yiwuwa.

Sun ce babu wani bil'adama da zai iya zuwa inda duniyoyin suke, nan da wani lokaci mai tsawo, domin suna da nisan daruruwan shekaru daga inda haske yake.