Pakistan ta dakatar da kashe wani matashi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shafqat ya yi kisan kai ne bada gangan ba yana da shekaru 14

Gwamnatin kasar Pakistan ta dakatar da aiwatar da hukuncin kisa a kan mutumin da aka samu da laifin aikata kisan kai bada ganganba shekaru goma da suka gabata.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yin korafin cewa an ganawa Shafqat Hussain ukuba lokacin yana shekaru 14 da haihuwa har sai da ya amsa laifi a wata kotun shari'ar laifukan ta'addanci.

Shafqat Hussain yana da 14 da haihuwa lokacin da aka same shi da laifin aikata kisan kai dake da alaka da ta'addanci shekaru 10 da suka gabata.

A ranar juma'a mai zuwa ne aka shirya kashe shi.

Kasar Pakistan, ita tafi kowacce aduniya yawan fursinonin dake jiran hukuncin kisa, da yawansu yanzu yakai 8261.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata ne kasar ta sake dawo da aiwatar da hukuncin kisa bayan kisan da akayi wa daliban wata makaranta a Peshawar a watan Desamba.