Sony ya yi Allawadai da kutsen da aka yi masa

Fim din The Interview Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fim din na kamfanin Sony ya yi shagube ne akan yadda aak shirya kashe shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa.

Kamfanin Sony Pictures ya yi Allawadai da abin da ya kira kutsen satar bayanai mafi muni da aka taba yi a tarihin kamfanin, lamarin da ya janyo tsaikon haska sabon fim din kamfanin mai suna The Interview a turance.

Shugaban kamfanin Sony Kazou Hirai shi ya bayyana hakan a wani taron tallata kayan laturoni na kamfanin, da aka gudanar a birnin Las Vegas na Amurka.

Mr Hirai ya kara da cewar ya na alfahari da wadanda suka tsaya tsayin daka, tare da jajircewa wajen ganin an haska fim din a gidajen silimar Amurka a lokacin bukukuwan kirsimati duk kuwa da barazanar da masu satar bayanan su aka yi wa kamfanin na Sony.

A watan da ya gabata ne dai wata kungiya ta masu kutse da ake kira The Guardians Peace hacker sukai kutsen satar bayanan kamfanin Sony Pictures, domin dakatar da shi haska sabon fim din barkwanci da ya yi shaguben yadda aka shirya kashe shugaba Kim Jong-un na kasar Korea ta Arewa.

Amurka ta zargi gwamnatin Korea ta Arewa da wannan satar bayanai, zargin da Korea ta Arewar ta musanta.

A bangare guda kuma rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin na Sony ya kashe akalla dalar Amurka miliyan 45 wajen shirya fim din The Interview.