An fara jarraba maganin Ebola a Liberia

Image caption Masana na cigaba da bincike kan maganin cutar Ebola

An fara jarraba wani maganin cutar Ebola a wata cibiya ta Doctors without Boarders a Monrovia.

Ana dai jarraba maganin ne a kan wasu majinyata bisa amincewarsu, yayin da ake ba wadanda suka ki amincewa da gwajin kyakkyawar kula.

Masu jagorancin binciken, wadanda masana ne daga jami'ar Oxford sun bayyana cewa za a samu sakamakon binciken nan da wasu watanni kalilan.

A watan Disamba ne aka fara nazarin wani maganin irin wannan mai suna Faviravir a kasar Guinea.

Cutar Ebola dai ta halaka sama da mutum 8000 bayan barkewarta a kasashen Liberia da Guinea da kuma Saliyo.