Farashin mai na ci gaba da faduwa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Farashin man fetur na ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya

Farashin man fetur ya koma kasa da dala 50 kan kowacce gangar danyan mai, a karon farko tun watan Mayun 2009.

A yanzu haka farashin man ya yi kasa da kaso goma, sabanin yadda aka sayar da shi a ranar Lahadi.

Masu sharhi sun ce farashin zai ci gaba da faduwa sakamakon yawan man da ake samarwa.

Tuni dai aka fara samun matsaloli a tattalin arzikin duniya yayin da kasashe masu arzikin man fetur suka ki rage yawan man da suke hakowa, lamarin da ya jawo cunkoso a kasuwar mai ta duniya.

Wasu dai na cewa man -- wanda a watan Yuni ake sayar da shi dala 110 kan ganga daya -- zai iya faduwa kasa warwas, har ma ya kai dala 20.