Ebola: Kenya ta tura ma'aikatan lafiya 170

Kenya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikatan za su kwashe watanni shida suna aiki

Kimanin ma'aikatan lafiya 170 na kasar Kenya za su isa kasashen Saliyo da Laberiya a yau Jumma'a.

Wannan wani mataki ne na kokarin da kungiyar tarayyar Afirka wato AU ta ke yi, don shawo kan matsalar cutar Ebola a yankin Afirka ta yamma.

Ma'aikatan, za su hadu da sauran takwarorinsu na sa- kai da aka tattaro daga kasashe 47.

Ana kuma sa ran za su gudanar da ayyukan kiwon lafiya har na tsawon watanni shida a kasashen biyu.