An kaddamar da farautar masu harin Faransa

France Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan uwan juna Sa'id Kouchi da Sharif Kouchi da suka kai harin Charlie Hebdo

'Yan sanda a Faransa, sun kaddamar da neman mutane nan biyu da ake zargi da kitsa harin da aka kai a kamfanin mujallar Charlie Hebdo.

Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 ciki har da edtian mujallar da wasu 'yan sanda biyu.

An kaddamar da neman Sa'id Kouchi da dan uwansa Sharif Kouchi bayan da aka fitar da hotunan su.

Bayanai sun ce wani mutum na uku da ake zargi mai suna Hamyd Mourad ya mika kansa ga 'yan sanda, bayan da aka wallafa sunansa a shafukan sada zaumunta.

Sai dai wasu daga cikin abokanansa sun ce ya na makaranta a lokacin da aka kai harin.

A baya mujallar ta Charlie Hebdo ta sha suka daga Musulmi da dama, bayan da ta yi wasu zane dake nuna batanci ga addinin Islama.